Harin ƙaramar hukumar Gwarzo: Sanata Barau ya yaba da gaggawar martanin tsaro, ya nemi kawo ƙarshen kutse na ƴan bindiga

Barau I. Jibrin 750x430

Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yaba wa jami’an tsaro kan ceto mutane uku daga cikin biyar da ’yan bindiga suka sace a ƙauyen Zurin Mahauta da ke garin Lakwaya, a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, a daren Lahadi.

Rahoton ya nuna cewa ’yan bindigar da ake zargin sun fito daga jihohin makwabta sun kutsa cikin ƙauyen, inda suka yi awon gaba da mutane biyar, lamarin da ya tayar da hankula a yankin.

Sanata Barau, ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya bukaci jami’an tsaro su ci gaba da bin sahun masu laifin tare da ceto sauran mutane biyu da ke hannunsu, yana mai jaddada cewa dole ne a hukunta masu aikata laifin.

Ya kuma bayyana cewa samun damar ceto mutane uku daga cikin biyar alama ce ta ƙoƙari da jajircewar jami’an tsaro, yana ƙarfafa su su ƙara ƙaimi domin tabbatar da dawowar sauran mutanen lafiya.

Labari mai alaƙa: Sojoji sun ceto mutane 3 da aka sace a Kano

A wani rahoto da aka wallafa a internet da misalin ƙarfe uku na rana, an ambato Kyaftin Babatunde Zubairu, mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin ƙasa ta Bataliya na uku, yana tabbatar da cewa an riga an ceto mutane uku.

Sanata Barau, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalisar dokokin kungiyar raya yankin tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka, ya jaddada cewa dole ne a dakatar da kai hare-hare a ƙauyukan Kano, yana mai kiran jami’an tsaro su ƙara tsaurara matakan tsaro da sa ido, tare da tabbatar da cewa tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne babban abin da ya fi muhimmanci.

Ya kuma tabbatar da ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da kayan aiki domin ƙara inganta aikinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here