Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sallami Shugaban riƙo na Hukumar Tattara Haraji Michael Ango.
Sanarwar ta fito ne daga Babban Mataimaki na Musamman ga Minista kan Sadarwa da Harkokin Zamani, Lere Olayinka, a ranar Juma’a.
Bayan sallamar Ango, jami’in da ya fi kowa girma a FCT-IRS an umarce shi da ya dauki ragamar jagorancin hukumar nan take a matsayin shugaban wucin gadi.
Sai dai ba a bayyana dalilin wannan mataki ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
Tun a ranar 9 ga Agusta, 2024, Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Ango a matsayin Shugaban riƙo na FCT-IRS, kuma a karkashin jagorancinsa, hukumar ta tara Naira biliyan 262 a shekarar 2024, wadda ta wuce burinta na Naira Biliyan 250, kuma ta fi kudaden da ta tara a shekarar 2023 na Naira Biliyan 211.1.













































