A bada izinin bincike kan takardar NYSC ta Tunji-Oja cikin gaskiya kuma a bayyane – Kungiyar al’umma

Olubunmi Tunji Ojo 750x430

Ƙungiyar kare gaskiya ta ƙasa mai suna Nigeria Integrity Movement (NIM) ta roƙi shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya ba da damar gudanar da bincike cikin gaskiya a bayyane kan takardar kammala hidimar ƙasa ta tsohon Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo.

Ƙungiyar ta ce ɓoye gaskiya a kan lamarin zai iya lalata amincin gwamnati da kuma bai wa ‘yan adawa damar yin amfani da batun wajen cin moriyar siyasa.

Jagoran ƙungiyar, Davies Ijele, wanda ya yi jawabi a Abuja, ya bayyana cewa kira daga wasu ƙungiyoyi na neman shugaban ƙasa ya kare ministan abu ne da ke iya cutar da martabar gwamnatin da ke ikirarin bin ƙa’ida da gaskiya.

Ya ce ko da minista na aiki yadda ya kamata, doka dole ta yi gaba da shi, kuma duk wani zargi na ƙirƙira ko rashin daidaito a takardu ya kamata a bincika cikin gaskiya.

Ijele ya nemi shugaban ƙasa ya ƙi matsin lamba daga masu son kare ministan, tare da buƙatar gudanar da cikakken bincike kan batun takardar NYSC ɗin sa.

Ya ƙara da cewa kasancewar Tunji-Ojo na daga cikin jami’an gwamnati masu aiki ba ya nufin yana sama da doka.

Ƙungiyar ta ce wannan kira ya biyo bayan rahoton da ya bayyana cewa akwai rashin daidaito a bayanan NYSC na ministan, inda aka ruwaito cewa an fara tura shi NYSC a 2006, amma ya tsere daga hidimar, daga baya aka sake tura shi a 2019, sannan takardar shaidar sa ta fito ne a 2023 bayan jinkirin buga ta.

Ijele ya ce bayanin da hukumar NYSC ta bayar ya bar wasu tambayoyi, musamman yadda mutum zai iya yin hidimar NYSC tare da sauran ayyukan gwamnati a lokaci guda.

Saboda haka, ƙungiyar ta nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa don gano ainihin inda aka samu kura-kurai.

Ya yi gargadin cewa yunkurin ɓoye gaskiya zai iya lalata sunan gwamnatin Tinubu da ikirarin ta na yaƙi da cin hanci.

Ya kuma tuna cewa a baya wani minista ya yi murabus saboda irin wannan matsala, yana mai cewa gaskiya da buɗaɗɗen bincike ne kawai za su kare martabar gwamnati.

A gefe guda kuma, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ribas ta karyata zarge-zargen da ke yawo a kafofin sada zumunta, tana mai cewa wasu ‘yan siyasa ne ke ƙoƙarin bata sunan ministan, wanda aikinsa ya fi ƙarfin duk wata farfaganda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here