Bugaje ya musunta kalaman Obasanjo kan yin wa’adi na uku

R L Olusegun Obasanjo and Usman Bugaje 750x430

Masanin siyasa kuma tsohon ɗan majalisar tarayya, Dakta Usman Bugaje, ya karyata musun tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo kan batun neman wa’adi na uku, inda ya ce tsohon shugaban ya yi duk mai yiwuwa domin tsawaita zamansa a mulki.

Obasanjo ya yi wannan batun ne a taron tattaunawar dimokuraɗiyya da cibiyar Goodluck Jonathan Foundation ta shirya a Ghana makon da ya gabata, inda ya ce: “Ba wawa ba ne ni.

“Da na so wa’adi na uku, zan iya samun sa”. Cewar Obasanjo.

Kuma babu ɗan Najeriya da ya rasu ko mai rai da zai ce na kira shi na ce masa ina son wa’adi na uku.”

Sai dai Bugaje, a wata hira da ya yi a shirin “Morning Show” na gidan talabijin Arise a ranar Litinin, ya ce su a majalisar dokoki lokacin mulkin Obasanjo sun shaida kai tsaye cewa akwai shirin wa’adi na uku.

Ya bayyana cewa: “Zan tabbatar maka da cewa Obasanjo ya nemi wa’adi na uku, ya yi duk abin da zai iya domin cimma hakan, amma bai yi nasara ba.”

Tsohon ɗan majalisar ya ce musun Obasanjo ba ya da hujja, yana mai ƙara da cewa wakilan Obasanjo sun yi barazana ga ’yan majalisa da dama a wancan lokaci.

Ya ce: “Ba wai saboda bai kira wani a waya ya gaya masa haka ba, shi ya sa za a ce bai nema ba.

Amma mu a majalisar mun san babu ko tantama cewa ya yi aiki dare da rana, kuma da yawa daga cikimmu an yi mana barazana ta hannun wakilansa.”

Labari mai alaƙa: Idan ina so na yi wa’adi na uku, da zan samu — Cewar Obasanjo

Bugaje ya kuma tunatar da wani lamari da ya faru da Sanata Victor Lar, shugaban tawagar Arewa a majalisar wakilai a lokacin, wanda ya ce an tilasta masa yin ɓoye a lokuta daban-daban kafin babban taron da suka yi na dakile shirin wa’adi na uku.

Ya ce: “Waɗanda suka rarraba kuɗi suna nan da rai, waɗanda suka karɓa suna nan da rai, waɗanda suka ƙi karɓa ma suna nan da rai. Shaida ta isa akwai, wannan lamari ba za a iya musawa ba.”

A shekarar 2006 ne batun wa’adi na uku ya mamaye siyasar Najeriya, lokacin da aka kawo kudirin sauya kundin tsarin mulki na 1999 domin bai wa shugaban ƙasa damar yin wa’adin mulki uku a jere.

Ana ganin cewa magoya bayan Obasanjo ne suka ɗauki nauyin wannan ƙudiri, a daidai lokacin da yake kammala wa’adinsa na biyu.

Sai dai bayan muhawara mai zafi a majalisar dattijai da ta wakilai, kudirin bai samu nasara ba, inda kungiyoyin farar hula, jam’iyyun adawa da ma wasu daga cikin jam’iyyar mulki ta PDP suka yi adawa da shi, suna masu cewa hakan zai lalata tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Rashin cin nasarar wannan kudiri ya kawo ƙarshen jita-jitar neman wa’adi na uku, wanda daga bisani ya buɗe hanyar da ta kai ga zaben 2007 da ya haifar da nasarar marigayi Umaru Musa Yar’Adua a matsayin shugaban ƙasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here