Na bar ofis da kadarorin da nake da su kafin zama na shugaban kasa – Buhari

Buhari APC NEW

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya bar fadar shugaban kasa da kadarorin da ya mallaka kafin ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2015.

A cewar wata sanarwa da Garba Shehu, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai ya fitar, Buhari ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da mambobin kungiyar gwamnoni a gidansa da ke Kaduna.

Ya ce ya kamata gwamnonin jihohi su rungumi tsarin mulki da ya shafi ‘yan kasa tare da mayar da bukatun jama’a a zuciyarsu da manufofinsu da shirye-shiryensu.

Ya ce dole ne shugabanci ya daidaita tsakanin tunkarar kalubale da kuma amfani da damar da za a samu wajen ciyar da kasa gaba.

Ya ce gwamnonin su fifita jin dadin jama’a a kan bukatun kansu.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana amincewa da ci gaban da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC ke samu.

Buhari ya godewa gwamnonin bisa ziyarar da suka kai masa, inda ya ce yayin da ya yi aiki da da yawa daga cikinsu, yanzu kuma wasu sababbi ne a gare shi.

Karin karatu: Ni amintaccen ɗan jam’iyyar APC ne — Buhari

Ya kuma nuna jin dadinsa kan gyaran gidansa na Kaduna da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi.

Gwamnan Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin Hope Uzodimma, ya mika godiya da girmamawar gwamnonin ga Buhari kan irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ga dimokradiyyar Najeriya da kuma jam’iyyar APC.

Ya yaba da rawar da Buhari ya taka wajen kafa jam’iyyar APC, inda ya kara da cewa gadon tsohon shugaban kasar na ci gaba da zayyana makomar jam’iyyar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here