A yau Lahadi ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya bi sahun Musulmai a filin Sallar Idi na kasa da ke kan titin filin jirgin sama a Abuja, domin gudanar da Sallar Eid-el-Fitr da ke nuna karshen watan Ramadan
Tinubu wanda ya isa wurin ne da mintuna kadan kafin karfe tara na safe, ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati, malaman addini, da sauran manyan baki.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, na daga cikin wadanda suka halarci taron idin.
A ranar Lahadi da yamma, shugaban kasar zai karbi baki a fadar gwamnati a karon farko tun bayan hawansa karagar mulki domin cin abincin rana don bikin Eid-el-Fitr.
Karin karatu: Hotuna: Yadda aka gudanar da Sallar Idi a fadar Sarkin Kano da ke Nassarawa
Sannan ya gudanar da bukukuwan baya a gidansa na Ikoyi dak e Legas.










































