Kotu Ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Dan, China, yankewa, hukuncin, kisa, rataya, ummita, frank
Babbar kotun jihar Kano, ta yankewa dan kasar China Frank Geng Quarong da ya kashe matashiyar nan Ummita hukuncin kisa ta hanyar rataya.Mai Shari’a Sunusi...

Babbar kotun jihar Kano, ta yankewa dan kasar China Frank Geng Quarong da ya kashe matashiyar nan Ummita hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke masa hukuncin bayan tabbatar da hujjojin da masu gabatar da kara suka yi a gaban kotun.

Karin labari: CBN na sayar da Dala 10,000 ga kowacce BDC kan Naira 1,251/$1

Idan dai za’a iya tunawa SOLACEBASE ta rawaito tun a ranar 16 ga watan satumbar shekarar 2022 ne Frank Geng, ya hallaka Ummita a Unguwar Jambulo da ke jihar kano.

Ummita dai budurwa ce ga Frank da suka shafe tsawon shekara da shekaru suna soyayya da juna kafin sabani ya gifta tsakaninsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here