Atiku Ga Shugabannin Afirka: Ku Kakkabe Dalilan Kawo Juyin Mulki, Ba Dakushe Alamomin Ba.

Atiku Abubakar 750x430

Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugabannin Afirka da su mayar da hankali kan abubuwan da suke haddasa yawaitar juyin mulkin da akeyi a nahiyar a baya-bayan nan, ba wai magance alamomin ba.

Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na X (wato Twitter) a ranar Alhamis yayin da yake mayar da martani game da juyin mulkin da aka yi a Gabon kwanan nan – na takwas a Afirka tun 2020.

Ya ce juyin mulkin da aka yi a gundumar Afirka ta Tsakiya abin Allah wadai ne, yana mai cewa kamata ya yi a yi duk mai yiwuwa don dorewar dimokradiyya a nahiyar.

“Na yi tir da juyin mulki a Gabon. Dimokuradiyya da mulkin dimokuradiyya sun tsaya a matsayin tsarin mulkin da aka fi so, don haka a yi duk mai yiwuwa dan dorewarta.

“Kamar yadda na ba da shawara game da Jamhuriyar Nijar, ya kamata ECOWAS da hukumomin Tarayyar Afirka su bude kofar huldar diflomasiyya da za ta bude shafin dakarun soji su koma barikin su.

“Yin juyin mulkin na baya-bayan nan ya kawo adadin mamayar da sojoji suka yi a tsakiyar Afirka zuwa 8 tun daga shekarar 2020.

“Ya zama wajibi mu mai da hankali wajan magance bazaranar juyin mulkin, ba wai dakushe alamun da ke haifar da juyin mulkin ba,” ya rubuta.

Hambararren shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, ya fuskanci zarge-zargen magudin zabe da kuma almundahana tun bayan da ya fara mulkin kasar mai arzikin man fetur kusan shekaru 14 da suka gabata.

Bayan juyin mulkin, an ga mazauna babban birnin kasar sun fantsama kan tituna suna murna tare da rungumar sojoji a kan titi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here