Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya N2m ga mutanen da aka yi yunƙurin rusawa gidaje

One of the buildings at Salanta in Kano marked for demolition
One of the buildings at Salanta in Kano marked for demolition

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta umurci gwamnatin jihar da sauran wadanda aka yi ƙara, su biya wasu mazauna unguwar Salanta, kudi naira miliyan ɗaya kowannensu akan yunƙurin rusa musu kadarori ba bisa ƙa’ida ba.

Alkalin kotun, Mai shari’a Simon Amobeda ya yanke hukuncin cewa yunƙurin gwamnatin Kano da jami’anta na sanya wa gidan Saminu Shehu Muhd ​​da na Tasiu Shehu Muhd ​cikin ​jerin gidajen da za a iya rushewa bayan an buga musu lambar jan fenti ba tare da bin ƙa’ida ba, tauye ƴancinsu ne na mallakar kadara kamar yadda sashe na 43 da 44 na tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tabbatar musu.

Jaridar Daily Trust ta ambato Barista Bashir Ibrahim, wanda ya shigar da karar a madadin Saminu da Tasiu, bayan yanke hukuncin yana yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya bayyana hakan a matsayin wata alama ta kare haƙƙi da martaba ƙimar ɗan’adam.

A nasa bangaren, lauyan gwamnatin jihar Kano da sauran waɗanda aka yi ƙara a shari’ar, Barista Musa Dahuru Muhd ​​daraktan shari’a a ma’aikatar shari’a ta Kano ya ce za su yi nazari a kan hukuncin tare da bai wa gwamnati shawara game da mataki na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here