Gwamnatin Bauchi ta kore sarakunan gargajiya 6 sakamakon zargin su da yin bangaranci a siyasa

Bala Mohammed 750x430
Bala Mohammed 750x430

Gwamnatin jihar Bauchi ta kori sarakunan gargajiya 6 sakamakon zargin su da yin bangarin a siyasa da kuma aiktata laifika da dama.

Sarakunan gargajiyar da abin ya shafa sun fito daga masarautar Bauchi da kuma masaratar Katagum.
Sanarwar korar tasu na cikin wata sanarwa da mukaddashin kamashinan kanan hukumomi na, Nasiru Ibrahim ya fitar sanan kuma ya rabawa manema labarai a Bauchi.
Sanarwar ta ce “Ma’aikatar kanan hukumomi ta amunce da korar sarakunan gargajiya 6 a masarautar Bauchi da kuma masarautar Katagum, sakamakon shiga siyasa, karay dokokin aiki, da kuma al’mun dahana da dukiyar al’umma da sauran su.”
“Wadan da abun ya shafa sun hada da Alhaji Aminu Muhammad Malami, dakacin Udubo, sai Alhaji Bashir Kabir Umar dakacin Azare, sai Umar Omar mai unguwar Gadiya, da kuma Umar Bani mai unguwar Tarmasawa, wadan da dukan su suna karkashin masarautar Katagum.” Inji sanarwar.
Sanawar ta kara da cewa “Sai wadan da abun ya shafa a masarautar Bauchi sune Bello Suleman, mai unguwar Beni sai kuma Alhaji Yusuf Aliyu Badara mai unguwar Badara.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here