Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocin sa da su ci gaba da rike mukamansu har zuwa ranar karshe ta gwamnatinsa.
Shugaba Buhari zai mika wa zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Rahotannin sun nuna cewa an samu jita jitar cewa shugaban ya rusa majalisar ministocinsa a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ya gudana a yau.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwar, Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai ya ce shugaba Buhari ya umurci dukkanin ministocin da su koma bakin aiki, su ci gaba da gudanar da ayyukansu.
“Labarin bogi da ake yadawa cewa an rushe Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ba gaskiya ba ne. An umurce mu da mu koma ofisoshinmu kuma ina da tabbacin za mu yi aiki har zuwa ranar 29 ga Mayu.













































