Wani matashi mai shekaru 24, Musa Abdullahi, ya banka wa gidan iyayen budurwarsa wuta saboda zargin ta yaudare shi.
Tuni dai matashin da ke zaune a Unguwar Riga Fada ta Karamar Hukumar Kumbutso a Jihar Kano, ya gurfana a gaban wata kotun majistare kan wannan lamari da ake zargin ya aikata saboda budurwarsa ta koma soyayya da wani mashinshininta.
Bayanai sun ce budurwar wadda aka sakaya sunanta ta samu raunuka a wasu sassan jikinta sanadiyyar wutar da masoyin nata ya cinna a gidansu.
Duk da cewa lauyan masu kara ya karanta kunshin laifin kan wanda ake tuhuma, sai dai matashin ya musanta zargin.
A halin yanzu kotun ta bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan Dan Kande har zuwa ranar 1 ga watan Yunin 2023 domin ci gaba da sauraron karar.
Aminya













































