Gwamnati ta haramta yin acaɓa a birnin Calabar

355336538 591706816467348 1622915462926537365 n
355336538 591706816467348 1622915462926537365 n

Gwamnatin jihar Cross River ta bayar da umarnin haramta duk wasu ayyukan acaɓa a ƙwaryar babban birnin Calabar.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan, Emmanuel Ogbeche ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa haramcin ya biyo bayan tattaunawa da shugabannin hukumomin tsaro a jihar.

A cewar sanarwar, an taƙaita ayyukan acaɓa ne a unguwannin gefe-gefen birnin ƙasar.

Gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana karya dokar, za a ƙwace babur din tare da hukunta wanda ya aikata laifin.

Gwamnatin jihar ta kuma yi gargadi a kan barnatar da dukiyoyin al’umma kamar fitulun kan hanya da masu bayar da hannu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here