Gwamnan CBN Ya Roki NLC Ta Janye Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Karancin Naira

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ranar Litinin ya roki ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ya rarrashi kungiyar kwadugo (NLC).

Emefiele ya bukaci Ngige ya taimaka ya sa baki NLC ta janye zanga-zangar da ta shirya farawa ranar Laraba mai zuwa a faɗin kasar nan. Idan baku manta ba ranar Jumu’an da ta shige, shugabannin NLC suka umarci dukkan mambobinsu su mamaye rassan CBN da ke faɗin Najeriya kan karancin tsabar kuɗi.

Amma a wani taron sirri da ya gudana a Shalkwatar ma’aikatar kwadugo da ke Abuja, an ji Emefiele na cewa zanga-zangar zata jiƙa wa CBN aiki idan ba’a dakatar da ita ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here