Ƴan majalisar wakilai 2 daga Kano sun fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC saboda rikicin cikin gida

Reps Reps 750x430

Wasu ‘yan majalisar tarayya biyu daga jihar Kano sun fice daga jam’iyyar (NNPP) sun koma jam’iyyar APC mai mulki, saboda rashin warware rikicin cikin gida a tsohuwar jam’iyyarsu.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya da Abdullahi Sani Rogo na mazabar Karaye/Rogo sun bayyana sauya sheka a zaman da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya jagoranta a ranar Alhamis.

Sauye-sauyen nasu ya kara dagula yawan ‘yan majalisar da ke tsallakawa jam’iyyar APC a watannin baya-bayan nan. Oluwole Oke, dan majalisar wakilai daga jihar Osun, shi ma ya koma jam’iyyar APC a wannan zaman.

Taron dai ya samu halartan shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje da wasu jiga-jigan jam’iyyar, wadanda suka halarci taron domin tarbar sabbin mambobin jam’iyyar.

A cikin ‘yan watannin nan dai majalisar ta samu sauya sheka da dama, wanda da yawa daga cikinsu sun karkata ga jam’iyyar APC mai mulki

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here