Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa sun dukufa wajen yin aiki tukuru domin yin nasara kan miyagu masu so su kashe Nigeria.
Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a matsayin babban bako na musamman a wajen taron tunawa da Sir Ahmadu Bello karo na 8 a ranar Talata a Kano.
“Wasu miyagu sun kudiri aniyar rusa tarihin da muka kafa a Arewa da Nigeria gaba daya, don haka ba zamu bari hakan ta faru ba in ji shi.
Farfesa Osinbajo ya kara da cewa cewa “yaki ne da muka kuduri aniyar samun nasara. Kuma mun san cewa da yardar Allah za a kawar da dukkan wadannan miyagun dakaru gaba daya”.
Don haka yake da kyau mu hada kai da masarautun gargajiya domin farfado da tarihin da magabatan kwarai suka bari.
A saboda haka ne “a lokuta da dama muke karfafa alaka tsakanin mu da masarautun gargajiya don wanzar da zaman lafiya da tsaro tare da inganta cibiyoyin gargajiya domin sune matakin farko na kariya ga sojojin da ke yaki da rashin tsaro.”
Ya kuma kara da cewa, wannan ya bayyana dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta kara zurfafa hadin gwiwa da masarautun gargajiya ta bangarori da dama, ya kara da cewa, “idan aka yi la’akari da yanayin muke ciki, cibiyoyin gargajiya na da muhimmanci ga shirinmu na aikin ‘yan sanda a fadin kasar nan, kuma za su iya isar da muhimman bayanai ga Jiha, da kuma hukumomin tsaro.”
Ya ba da tabbacin cewa “Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya. Yunkurin na baya-bayan nan ya mayar da hankali ne kan tura fasahar sa ido, tattara bayanan sirri da kai hari.
“Za kuma mu ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar shari’a ta tarayya, takwarorinsu na Jihohi, da jami’an tsaro, don tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda aka kama da laifin ta’addanci da kuma munanan laifuka.”
Daga nan sai Farfesa Osinbajo ya jaddada rawar da masarautun gargajiya ke takawa a matsayin wani ginshiki tsakanin al’umma domin magance kalubalen tsaro yadda ya kamata da kuma samar da zaman lafiya da hadin kai.












































