Gwamnatin tarayya ta rage kuɗin wankin Ƙoda daga naira dubu hamsin zuwa naira dubu goma sha biyu a kowane yi, wanda ya zama ragin kimanin kashi 76 zuwa 80 cikin ɗari a wasu manyan asibitocin gwamnati.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na sauƙaƙa wa ɗimbin ‘yan Najeriya da ke fama da cututtukan da suka shafi koda.
Asibitocin da ke amfana da wannan shiri sun haɗa da cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Ebute-Metta, Legas, cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Jabi, Abuja, da asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan.
Haka kuma akwai cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owerri, asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, da cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Abeokuta.
Sauran sun haɗa da asibitin koyarwa na jami’ar Legas, cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Azare, da asibitin koyarwa na jami’ar Benin.
Haka kuma shirin ya haɗa da asibitin koyarwa na jami’ar Calabar da asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Wannan shiri na cikin manufofin gwamnatin shugaba Bola Tinubu na “Sabon Fata”, wanda ke da nufin tabbatar da cewa ‘yan ƙasa suna samun ingantacciyar jinya cikin sauƙi.
A jihar Kano, wannan tallafi na kashi 80 cikin ɗari ya janyo ƙaruwa sosai a yawan marasa lafiya da ke zuwa yin wankin Ƙoda a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH).
Tare da wannan tsari, kuɗin jinya ya ragu daga tsakanin naira dubu hamsin zuwa sittin zuwa naira dubu goma sha biyu kacal, wanda ya sauƙaƙa wa marasa lafiya da ke da ƙaramin ƙarfi.
Daraktan ma’aikatan jinya a asibitin, Tijjani Rahim, wanda ke jagorantar sashen wankin Ƙoda, ya bayyana cewa yanzu asibitin na karɓar marasa lafiya daga mutane 22 zuwa 25 a kowace rana, sakamakon wannan tallafi.
Haka kuma shugaban asibitin, Farfesa Abdurrahman Sheshe, ya tabbatar da cewa shirin ya fara aiki, inda asibitin ya karɓi kayan aiki don gudanar da shirin.
Sheshe ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da shirin gaggawa na lafiya da ambulan na ƙasa (NEMSAS) a asibitin, wanda ke bayar da agajin jinya kyauta na awanni 48 ga mata masu juna biyu, yara, waɗanda suka samu haɗura da sauran masu buƙatar taimako cikin gaggawa.
Ya kuma roƙi ma’aikatar lafiya ta tarayya da masu hannu da shuni su taimaka wajen ci gaba da wannan shiri.
Wannan tallafi na wankin Ƙoda wani ɓangare ne na sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa a fannin lafiya, ciki har da shirin tallafin asusun kula da lafiya na asali (BHCPF) da shirin NEMSAS, da nufin rage nauyin kuɗin jinya a kan ‘yan ƙasa da kuma inganta tsarin kula da gaggawa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, a ranar 21 ga watan Agusta, 2025, gwamnatin tarayya ta amince da wannan shirin tallafin wankin Ƙoda ga asibitoci 11 na tarayya da ke cikin sassan ƙasar nan guda shida.
















































