Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Rome

Tinubu depart new

Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar Abuja gobe Lahadi zuwa birnin Rome, babban birnin ƙasar Italiya, domin halartar taron shugabannin ƙasashe da gwamnatoci mai taken “Aqaba”

An shirya taron ne domin mai da hankali kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin yammacin Afirka.

Taron zai fara a ranar 14 ga watan Oktoba, kuma zai haɗa shugabannin ƙasashe, manyan jami’an leƙen asiri da na tsaro daga ƙasashen Afirka, da kuma wakilai daga ƙungiyoyin gwamnati da na ƙasa-da-ƙasa domin tattauna sabbin ƙalubalen tsaro da ke fuskantar yankin.

Taron “Aqaba” wata manufa ce da aka ƙaddamar a shekarar 2015 ƙarƙashin jagorancin Sarkin Jordan, Abdullah na II, domin yaƙar ta’addanci.

Ƙasar Jordan da gwamnatin Italiya ne ke jagorantar shirin tare.

Shirin yana mayar da hankali kan rikice-rikicen tsaro da ke damun yammacin Afirka, musamman yaduwar ƙungiyoyin ta’addanci, haɗin kai tsakanin masu aikata laifuka da ‘yan ta’adda, da kuma haɗuwar ta’addancin ƙasa da ƙasa da fashin teku a yankin Gulf of Guinea.

A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa mahalarta taron za su tattauna hanyoyin haɗa kai tsakanin ƙasashe da ƙungiyoyin duniya wajen magance matsalolin tsaro da ke da nasaba da iyakoki.

Haka kuma za a tsara dabarun yaƙi da ta’addanci a ƙasa da teku, tare da hanyoyin dakile yada akidar ta’addanci ta intanet da shafukan sada zumunta.

Baya ga halartar taron, shugaba Tinubu zai gudanar da ganawa ta musamman da wasu shugabannin ƙasashe domin tattauna hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro da ke ƙaruwa a yankin.

Shugaban ƙasar zai samu rakiyar karamar ministar harkokin ƙasashen waje, jakadiya Bianca Odumegwu–Ojukwu; ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; mai ba da shawara na musamman kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da darakta janar na hukumar leƙen asirin ƙasa, jakada Mohammed Mohammed, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here