Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya koma APC

Ramalan Yero, tsohon, gwamna, kaduna, APC
sohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya koma jam'iyyar APC, watanni kaɗan bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP. Ramalan Yero ya sanar da ficewar...

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya koma jam’iyyar APC, watanni kaɗan bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Ramalan Yero ya sanar da ficewar tasa ne a wani bayani da ya yi wa manema labaru, yau Litinin a garin Kaduna.

A bayanin nasa, tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce ya koma APC ne bisa dalilai na ƙashin kansa bayan ya tattauna da waɗanda ke kusa da shi a harkar siyasa.

Karanta wannan: ‘Yan Tunisiya sun ɓace a teku bayan yunkurin shiga Italiya

A cikin watan Oktoban shekarar 2023 ne Yero ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Ramalan Yero ya riƙe gwamnan jihar Kaduna ne ƙarƙashin jam’iyyar PDP daga shekara ta 2012 zuwa 2015 bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Patrick Yakowa a wani hatsarin jirgin helikwafta.

Daga nan ne ya yi takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ta PDP sai dai bai yi nasara ba.

Daga baya Ramalam Yero ya sha yunƙurin sake yin takarar gwamnan jihar, amma bai samu nasarar hakan ba, inda ya gaza yin nasara tun a matakin zaɓen fitar da ɗan takara.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here