Kasar Amurka ta amince da siyar da kwayar zubar da ciki, ta mifepristone a mahada da shagunan saida maghnguna.
Ana shan Mifepristone a hade tare da wani magani da ake kira misoprostol don kawo karshen ciki a cikin makonni goma kwana 70 ko ƙasa da haka tun daga ranar farko na hailar ƙarshe na mai juna biyu
Hukumar kulada Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta amincewa da maganin a cikin shekara ta 2000 amma marasa lafiya za su iya samun ta ashaguna.
A ranar Talata ne dai, hukumar ta sabunta shafin yanar gizon ta tare da sabbin abubuwan da ake buƙata don maganin, tana mai cewa “ana iya ba da shi ta hanyar ingantattun magunguna ko ta ko ƙarƙashin kulawar ƙwararrun likitoci”.
Rahotanni sun ce ana buƙatar takardar sayan magani wannan sabuwar sabuwar doka.
Hukumar ta ce an cimma wannan matsayar ne bayan gudanar da bita na tantance hadarin da dabarun magance matsalar.
An ce wannan matakin wani yunƙuri ne da gwamnatin shugaba Joe Biden ta yi na kare haƙƙin zubar da ciki biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na soke haƙƙin zubar da ciki, tare da hana wasu jihohi.
Mata a jihohin da aka haramta zubar da ciki za su bukaci yin balaguro zuwa wasu jihohin domin samun maganin zubar da ciki.













































