Kano: Peter Obi ya ziyarci wadanda harin masallaci ya ritsa da su a Gezawa

Peter Obi, ziyarci, kona, masallaci, gezawa, larabar, abasawa, jihar, kano
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi a ranar Lahadi ya ziyarci wadanda aka kona a masallaci a yankin Larabar...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi a ranar Lahadi ya ziyarci wadanda aka kona a masallaci a yankin Larabar Abasawa a Karamar Hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Peter Obi da isowarsa, kai tsaye daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano ya tafi asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ke karbar magani.

Karin labari: Hukumar NDLEA Ta Bayyana Neman Wasu Ma’aurata Ruwa A Jallo, Ta Kuma Kama Masu Siyarda Hodar Iblis 4

Ya ce, “Wannan abu ne mai ban tsoro kuma har yanzu abin la’akari ne sosai. Abin bakin ciki ne wannan na iya faruwa a kasarmu a yau.

“Babu wanda zai iya cewa dalilin da yasa wannan yaron zai iya yin irin wannan abu ga danginsa da al’ummarsa.

“Muna ci gaba da yin Allah wadai da irin wannan aika-aikar a kan mutane. Dalilina na zuwa nan shi ne don in nuna cewa hadin kai da goyon baya a cikin kulawar su ta wata hanya da kuma masu kula da asibitoci a cikin abin da suke yi da kuma sake yin Allah wadai da wannan mummunan ta’asa na rashin hankali.”

Karin labari: Gwamnatin Kano ta sake nanata dokar haƙar yashi da ma’adanai ba bisa ka’ida ba

Don haka Peter Obi ya jajantawa gwamnati da al’ummar Kano, sannan ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai don yakar irin wannan aikin na rashin hankali.

Idan dai za’a iya tunawa rikicin dangi kan rabon gadone ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a unguwar Larabar-Albasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Karin labari: Jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Iran ya yi hatsari

An ce matashi, Shafiu Abubakar, ya bankawa wani masallaci wuta ne a lokacin da masu ibada ke gudanar da sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe.

Wanda ake tuhumar ya bankawa masallacin wuta ne da man fetur, inda ya kulle kofar wanda hakan ya zama sanadin rasa rayukan wasu daga cikin al’umma tare da jikkatar a kalla mutum 40.

A cewar hukumomi kimanin mutane 14 da lamarin ya shafa ne suka mutu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here