Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya bude iyakoki

Tinubu, bude, iyakoki, najeriya, nijar
Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar. Ya kuma dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan...

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin bude iyakokin Najeriya ta kasa da ta sama da Jamhuriyar Nijar. Ya kuma dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya aikewa manema labarai.

Ya ce wannan umarnin ya yi daidai da shawarar da hukumar ta ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta gudanar a ranar 24 ga watan Fabrairun 2024 a Abuja.

Karin labari: Da Dumi-dumi: Najeriya ta bude kan iyakokinta da Nijar

“Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin tattalin arziki da suka kakabawa Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso da kuma Guinea” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa “Shugaban kasa ya ba da umarnin a dage takunkumin da aka sanyawa Jamhuriyar Nijar nan take.”

A cewar Ngelale “Na daya Rufe iyakokin kasa da ta sama tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama na ECOWAS a duk jiragen kasuwanci da ke zuwa ko kuma daga Jamhuriyar Nijar.

Karin labari: Hukumomin Tigray na ƙasar Habasha sun ce an kori tsoffin ‘yan tawaye 100,000

Na biyu dakatar da duk wani hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Najeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu hada-hadar hidima da suka hada da ayyukan amfani da wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar.

Na uku daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar a babban bankin ECOWAS da kuma daskarar da kadarorin Jamhuriyar Nijar, da kamfanonin gwamnati da ma’aikatu a bankunan kasuwanci.

Karin labari: Dakarun Djibouti sun fice daga tsakiyar Somaliya saboda rikicin cikin gida

Na hudu dakatar da Nijar daga duk wani tallafi na kudi da mu’amala da duk hukumomin kudi musamman EBID da BOAD.

Sai na biyar hana tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da ‘yan uwansu.

Shugaba Tinubu ya kuma amince da dage takunkumin kudi da tattalin arziki da aka kakabawa Jamhuriyar Guinea” in ji sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here