Wani babban jami’in gwamnatin Kano ya mayar da Naira Miliyan 4.7 ga asusun jihar bayan ta yi masa aringizon biyan bashi

WhatsApp Image 2025 01 29 at 00.08.10 685x430

Mataimakin shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano (REMASAB) Alhaji Lamir Mukhtar Hassan, ya mayarwa asusun gwamnatin jihar sama da Naira miliyan 4 da dubu dari 7, bayan ya gano an yi kuskuren biyansa bashin da yake bi.

Hassan ya bayyana cewa bashin da yake bi na Naira dubu 4,700,861.55 an biya shi tun a watan Disambar 2024.

Sai dai ya yi mamakin samun adadin kudin sama da yadda yake tsammani a asusunsa a watan Janairu.

Alhaji Lamir Mukhtar Hassan, ya shaida wa SolaceBase cewa da ya gane kuskure ne, sai ya mayar da kudaden zuwa asusun gwamnati a ranar Litinin.

Wannan hali na gaskiya da ba kasafai aka fita ganinsa ba, hakan ya sa ya samu yabo sosai, inda mutane da yawa ke yabawa Hassan bisa rikon amanar da ya yi a lokacin da ake fama da matsalar tattalin arziki.

A wata hira ta musamman da ya yi da SolaceBase, Hassan ya ce, “Kudin ba nawa ba ne, don haka ba ni da ikon ajiye su. Na mutanen jihar Kano ne kuma na mayar da shi ne domin gwamnati ta ci gaba da kokarin inganta jihar.”

Da yake ba da labarin lamarin, Hassan ya bayyana cewa, “Lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada ni, na fuskanci matsalar albashi wanda har zuwa watan Oktoba.

Alhaji Lamir Mukhtar Hassan, “An biya bashin wadannan watanni a watan Disamba. Amma a ranar 27 ga watan Janairu, na sake karbar wannan bashin, wanda na san kuskure ne,”.

Sai dai ya shawarci ma’aikata da su riƙe gaskiya da amana a ayyukan su domin ci gaban jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here