Uban Jami’ar Illorin Malam Habib Yazid ya rasu

unilorin new
unilorin new

Uban Jami’ar Ilorin Malam Habidu Yazid-Rafindadi ya rasu.

Daraktan sashen yada labarai na jami’ar Mista Kunle Akogun ne ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN rasuwar uban Jami’ar a ranar Alhamis.

Daraktan ya ce Rafindadi ya rasu ne a Abuja, amma ya ce har yanzu jami’ar ba ta bayar da wata sanarwa a hukumance kan rasuwarsa ba.

Kamfanin dillancin Labaran ya rawaito cewa marigayin wanda Dan jihar Katsina ne, ya kasance tsohon sakataren gwamnati kuma shugaban ma’aikata a tsohuwar jihar Kaduna.

An nada Rafindadi shugaban Hukumar Gudanarwa Kuma uban Jami’ar ta Illorin a Shekarar 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here