Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Yahaya Isa Bunkure a matsayin shugaban jami’ar ilimi ta tarayya da ke Zariya a jihar Kaduna.
Farfesa Bunkure sanannen malami ne wanda ya kware a fannin ilimin kimiyya, wanda kafin na shi ne shugaban kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce Tinubu ya kuma nada Abdurrazaq Abubakar Nakore, a matsayin uban jami’a da kuma shugaban majalisar gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta tarayya ta Yusuf Maitama Sule, Kano, yayin da Farfesa Abdullahi Tukur Kodage aka nada shi a matsayin mataimakin shugaban jami’ar.
Karin karatu: Inuwa Waya ya nuna damuwa kan karuwar ayyukan daba a Kano, ya yi kira da a inganta harkar ilimi
SolaceBase ta rawaito cewa Injiniya Nakore, dan Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya ne, kuma shi ne babban sakataren hukumar Lantarki ta Karkara a Jihar Jigawa.
Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya da Yusuf Maitama Sule Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano na daga cikin kwalejojin ilimi guda hudu da aka inganta zuwa cikakkun jami’o’i tsakanin 2022 zuwa 2023.
Dangane da dokokin gudanarwar cibiyar, mai ba da shawara zai yi aiki na tsawon shekaru hudu, yayin da mataimakan shugabannin za su yi aiki na shekaru biyar













































