Gwamnatin soji da ke mulki a Sudan ta ce za ta bari a shigar da kayan agaji ta Chadi da Sudan ta Kudu.
Gwamnatin ta haramta bi da kayan agaji ta Chadi inda ta zargi haɗaɗɗiyar daular larabawa, UAE da yin amfani da jerin gwanon motocin agaji da samar da makamai ga dakarun RSF. UAE dai ta musanta zargin yin hakan.
Karin labari: Majalisar dokokin Edo ta fara shirin tsige Shaibu
Clementine Nkweta-Salami, jami’ar MDD a Sudan ta ce matakin abin maraba ne kuma zai taimaka wajen isar da kayan agaji zuwa mutanen da ke tsananin buƙata.
Misis Salami ta ƙara da cewa gwamnati ta amince ta buɗe hanyoyin jirgi domin isar da kayan jin ƙai a Fasher da Kadugli da El Obeid.
Karin labari: An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara
Dubban mutane sun mutu, kusan miliyan takwas sun ɗaiɗaita a rikicin da aka shafe fiye da wata goma ana yi tsakanin dakarun da ba sa ga muciji da juna a Sudan.
Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya, WFP ya ce yaƙin na Sudan na iya ingiza mutane da dama cikin yunwa idan har ba a tsagaita yinsa ba.