Shugabannin Afirka za su shiga tsakani don warware rikicin Sudan

342518905 762817342082650 5082622002072961617 n
342518905 762817342082650 5082622002072961617 n

Shugabannin ƙasashen Afirka sun ce za su dauki hanyar zuwa Sudan, domin shiga tsakani don kawo karshen faɗan da ake gwabzawa tsakanin bangarorin da ke yaki da juna, da ya janyo mutuwar sama da farar hula 200.

An yi ta jin karar harbe-harbe duk da yarjejeniyar dakatar da wutar da aka cimma a jiya Talata.

Wakilin BBC ya ce tun ranar Asabar hau yau din nan, bangarorin biyu ke gwabza fada babu kakkautaba, ba alamun za su saduda bare su bada damar da za a kai agaji ga farar hula da fadan ya rutsa da su.

Kungiyar Tarayyar Afirka na fatan za a tsagaita domin shugaban Djibouti, da Kenya da Sudan ta Kudu su sauka kasar.

Ana fargaba kasar na gab da fadawa yakin basasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here