Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Gombe, Abdullahi Mai kano Umar ya bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
An ruwaito cewa, Mai kano ya bayyana barin NNPP tare da shiga APC ne bayan wata ganawa da ya yi da gwamnan jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a ranar Alhamis 2 ga watan Fabrairu da yamma.
Ya zuwa yanzu dai babu wasu bayanai da aka samu game da ganawar gwamnan da tsohon shugaban na NNPP, amma dai wannan babban ci gaba ne da gwamnan da ke neman a sake zabensa a jihar.













































