Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki zuwa jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.
A lokacin ziyarar shugaban zai kaddamar da bikin wasannin na sojojin ruwan kasar karo na 12.
Haka kuma ana sa ran shugaban zai kaddamar da sabon filin wasa da ke sansanin sojin ruwa na Ojo.













































