Hukumomin Saudiyya sun saki wasu ‘yan Najeriya uku da aka tsare a Jeddah tun watan da ya gabata bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq, bayan sun shafe kusan makonni huɗu a hannun jami’an tsaro.
Wannan nasara ta samu ne sakamakon tattaunawa mai zurfi da shugaban hukumar yaki da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), Janar Mohammed Buba Marwa (rtd), ya gudanar tare da shugabannin hukumar kula da miyagun ƙwayoyi ta Saudiyya (GDNC).
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati sun bayar da cikakken goyon baya domin ganin an tabbatar da adalci ga waɗannan matafiya.
Rahoton hukumar NDLEA ya bayyana cewa wata ƙungiya ta masu safarar miyagun ƙwayoyi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA), Kano, ta ɗaura sunayen waɗannan baƙi uku a kan jakunkunan da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi.
Wannan ya sa aka kama su a Saudiyya bayan sun isa Jeddah domin sauke aikin Umrah a ranar 6 ga watan Agusta, 2025.
Karin labari: NDLEA ta cafke mutum 6 bisa zargin saka kwaya a jakunkunan wasu yan Najeriya 3 da Saudiyya ta kama bayan zuwa umara
Bayan korafe-korafen da iyalan waɗanda abin ya shafa suka shigar, hukumar NDLEA ta fara bincike wanda ya kai ga cafke shugaban ƙungiyar, Mohammed Ali Abubakar wanda aka fi sani da Bello Karama, da wasu abokan harkallarsa uku.
Haka kuma an gano rawar da wasu jami’an jirgin suka taka a safarar miyagun ƙwayoyin, lamarin da ya tabbatar da cewa ba su da hannu a zargin da aka yi musu.
Da wannan hujjoji da aka gabatar, Marwa ya gudanar da jerin tattaunawa da takwarorinsa na Saudiyya a matakai daban-daban. Wannan ya haifar da sakin mutum na farko a ranar 14 ga Satumba, sannan sauran biyun a ranar 15 ga Satumba, 2025.
Da yake nuna farin ciki, Janar Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya da suka mutunta yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakaninsu da NDLEA.
Ya kuma jaddada cewa goyon bayan shugaban kasa Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa ba a hukunta wani ɗan Najeriya ba tare da laifi ba a ƙasashen waje.
Ya kuma gode wa ministan shari’a, ministan harkokin waje, ministan sufurin jiragen sama da mai ba da shawara kan tsaro na ƙasa bisa gudunmawarsu a wannan al’amari.













































