Saudiyya ta fitar da shirye-shiryen bada damar sayar da barasa ga jami’an diflomasiyyar da ba musulmi ba a karon farko, kamar yadda wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan shirin suka shaida wa AFP a ranar Laraba.
Haramcin sayar da barasa dai ya kasance cikin dokar kasar Saudiyya tun a shekarar 1952, bayan daya daga cikin ‘ya’yan Sarki Abdulaziz ya bugu, kuma a fusata ya harbe wani jami’in diflomasiyyar Burtaniya.
Karanta wannan: Saudiyya: za mu iya daidaita alaƙa da Isra’ila amma bisa sharaɗi
An kwashe shekaru ana ta yada jita-jitar cewa ana amfani da barasa a cikin masarautar ta Gulf a cikin sauye-sauyen zamantakewa da aka gabatar a wani bangare na ajandar kawo sauyi na Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, ciki har da bullo da gidajen sinima da bukukuwan kade-kade.
Karanta wannan: Gwamna Aiyedatiwa ya nada tsohon ma’aikacin Hukumar NASS mataimakinsa
Sanarwar da gwamnatin Saudiyya ta fitar a ranar Laraba ta ce hukumomi suna bullo da “sabon tsarin dok da nufin dakile haramcin cinikin barasa da kayayyakin da ofisoshin diflomasiyya ke shiga da su”.
A karkashin dokar Saudiyya, hukuncin sha ko mallakar barasa na iya kai mutum ga gidan yari hade da tara da bulala a bainar jama’a, da kuma korar baki yan kasashen waje daga kasar.