An wayi garin Laraba farashin litar fetur ya kai Naira 560 a gidajen mai a Kano, a wasu jihohin kuma har Naira 700.
An kuma samu samu dogayen layuka a gidajen man da Aminiya ta ziyarta a Kano, inda farashin lita ke kaiwa farawa daga Naira 350 zuwa 560.
Aminiya ta je gidan mai na AYM Shafa, inda ake sayar da lita a kan N560, gidan man Alhaji Alasan de ke Titin Gaida a Karamar Hukumar Kumbotso na sayarwa N450; A.Y. Maikifi, N400 daga N220 da ake sayarwa a safiyar Talata.
Platinum Oil Services, na sayarwa N380, sai B.A Bello, kuma a kan Naira 350, a yayin da Kanawa ke bayyana damuwa kan tashin gwauron zabon man da kuma dogayen layin da ake fama da shi a gidajen mai.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara samun karancin man da kuma dogayen layuka a sassan, bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar cewa biyan kudin tallafin mai da gwamnati ke yi ya zama tarihi a Najeriya.
Wani mazaunin Kano, B.A. Haruna Ishaq, ya bayyana damwa kan yadda gwamnatin ta shigo, inda ya ce ko a ranar Talata ya sayi lita a kan N210, amma zuwa ranar Laraba farashin ya koma N450.
Wata matar aure mai suan A’isha Aliyu, ta koka cewa wahalar man ta sa masu baburan A Daidaita Sahu sun yi kara kudi, inda yanzu kudin da take kashewa wajen kai ’ya’yanta makaranta ya karu daga N400 zuwa N550.
Aminiya ta tuntubin Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN), Reshen Jihar Kano, Bashir Dan-Mallam wanda ya ce za su yi taron gaggawa kan lamarin, kafin daga baya ya yi bayani.
Gwamnatin Tayyya ta sha alwashin hukunta masu neman kawo cikas ga cire tallafin man fetur, a yayin da masu bumburutu suka wasa wukarsu, bayan sabon shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar cewa biyan tallafin mai ya zama tarihi.
Tun bayan furucin na Tinubu a jawabinsa na karbar rantsuwar fara aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 a ranar Linintin, wasu gidajen mai suka dakatar da aiki, aka kuma fara samun dogayen layin ababen hawa.
Tinubu dai ya jaddada goyon bayan gwamnatinsa ga matakin da gwamnati mai barin gado ta Shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na soke biyan kudin tallafin mai da ke lakume tiriliyoyin kudade daga aljihun gwamnatin.
“Mun jinjina wa gwamnati mai barin gado game da soke biyan tallafin mai, wanda mawadata ne suka fi amfana da shi maimakon talakawa,” in ji Shugaba Tinubu.
Sa’o’i kadan bayan nan ne, tun a ranar Litin din, wasu gidajen mai suka rurrufe, wanda ya haddasa karanci da tsadar man a wasu sassan Najeriya.
Hakan ya sa farashin litar man ya yi tashin gwauron zabo zuwa Naira 700 a wasu wurare, a yayin da fasinjoji ke kokawa bisa ninka kudin mota da aka yi.
Kungiyoyin kwadago da jami’iyyun adawa dai na ganin cewa lokacin da shugaban kasar ya yi sanarwar bai dace ba.
Amma duk da haka, gwamnatin ta ce babu gudu, babu ja da baya kan cire tallafin, wanda ke lakume tiriliyoyin Naira a duk, shekara, alhali abin da talakawa ke amfana da shi a ciki bai taka kara ya karya ba.
Majalisar Wakilai ta jaddada cewa dokar kasafin kudin 2023 ba ware ko sisi ba domin biyan tallafin man, wanda gwamnatin ta bayyana a matsayin kara wa mai karfi karfi.
A yayin da gwamnatin ta lashi takobin hukunta masu neman kawo cikas ga cire tallafin, kungiyoyin dillalan mai sun yi maraba da matakin tare da cewa za su ba da hadin kai domin ganin ba a samu karancin mai ko tsadar da ta wuce misali ba.
(Aminiya)













































