Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tawagarsa a ranar Litinin din da ta gabata sun dawo gida bayan shafe mako guda suna ziyarar aiki a Masarautar Morocco bisa gayyatar Sarki Mohammed na biyar
Sarkin ya gudanar da tarurruka da jami’an kasar Morocco tare da ziyartar wasu manyan biranen kasar da wuraren tarihi da suka hada da Casablanca, Marrakech, Rabat da kuma Fes.
Solacebase ta samu rahoton cewa Mai Martaba ya karbi baƙuncinsa da kuma zuwa liyafar karramawa daga ma’aikatar kula da harkokin addini da albarkatu da kuma fitacciyar gidauniyar sarki Mohammed.
Sarkin ya kuma ziyarci Cibiyar horas da limamai da masu wa’azi da ke Rabat inda ya gana da shugabannin Cibiyar tare da neman karin tallafin karatu don taimaka wa matasanmu da sauran masu sha’awar ci gaba da karatu a wannan fanni.
Mai martaba ya kammala ziyarar tasa a Casablanca da wata ganawa da wasu gungun ‘yan Najeriya mazauna birnin da ke gabar teku, inda ya gargade su da su kasance masu bin doka da oda da kuma nuna kyawawan halaye a matsayinsu na Jakadun Najeriya.’’
A karshen ziyarar, mai martaba ya kasance babban bako na musamman a taron kasa da kasa da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco da gidauniyar sarki Mohammed suka shirya.
A sakonsa na fatan alheri, a yayin bikin, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira da a cigaba da hakuri, hadin kai da fahimtar juna kan muhimman batutuwan da suka shafi shugabannin addini da kuma dukkanin mabiya addinin Musulunci.













































