Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta ce akwai bukatar jami’anta su rike makamai wajen gudanar da ayyukansu, duba da irin kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar nan. Shugaban rundunar, Mista Dauda Biu ne ya bayyana haka a ranar Asabar a lokacin da yake kaddamar da jami’an rundunar su 1,762 da suka kammala karatunsu na tsawon watanni hudu a cibiyar horas da sojojin Najeriya (NATRAC) da ke Kontagora a Nijar.
Idan dai za a iya tunawa, a baya rundunar ta kai karar jami’anta da su dauki makamai domin kare lafiyarsu, kiran da hukumomi suka yi watsi da shi.