Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu hasken rana tare da ɗan hazo a sassan ƙasar daga ranar Lahadi zuwa Talata mai zuwa.
A sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Asabar a Abuja, ta bayyana cewa a ranar Lahadi za a sami sararin sama mai rana da ɗan hazo a yankunan Katsina, Yobe, Kano da Jigawa, yayin da sauran sassan arewa za su fuskanci cikakken hasken rana da safe.
Sai dai hukumar ta ce a ƙarshe na rana ko da yamma, ana sa ran guguwar ruwa mai ɗan ƙarfi a yankin kudancin Taraba, yayin da ake sa ran sararin sama mai haske tare da ɗan gizago da safe, sannan da yamma ko dare ana iya samun guguwar ruwa a wasu yankunan Benue da Kogi.
NiMet ta kuma bayyana cewa a kudancin ƙasar ana sa ran sararin sama mai gizago da kuma yiwuwar ruwan sama da asuba a yankunan Ebonyi, Ogun, Ondo, Imo, Abia, Legas, Rivers, Bayelsa, Cross River da Akwa Ibom, sannan da yamma ko dare za a iya samun ruwan sama mai ɗan ƙarfi.
A ranar Litinin, hukumar ta ce za a sami hasken rana a yankin arewa da safe, sannan da yamma za a iya samun guguwar ruwa a kudancin Kaduna da kudancin Taraba.
Za a sami sararin sama mai haske da gizago da safe, sannan da yamma a wasu yankunan Benue ta kudu, babban birnin tarayya Abuja da Nasarawa za a iya samun guguwar ruwa.
A kudancin yankin, NiMet ta ce za a sami gizagon sararin sama tare da yiwuwar ruwan sama da asuba a yankunan Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom, sannan da yamma ana iya samun guguwar ruwa mai ɗan ƙarfi a wasu sassan Enugu, Ogun, Oyo, Abia, Imo, da sauran jihohin kudu.
A ranar Talata kuma, hukumar ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun rana a arewa da gizago , yayin da a kudu za a sami ruwan sama da asuba a wasu yankunan Ogun, Legas, Cross River da Akwa Ibom, sannan da yamma a wasu sassan Ogun, Akwa Ibom, Rivers, Bayelsa, Delta, Cross River da Legas za a iya samun ruwan sama mai tsanani.
NiMet ta ja hankalin jama’a da su yi taka-tsantsan yayin tafiya a lokacin ruwan sama, musamman masu tukin mota, sannan ta shawarci manoma da su guji yayyafa taki ko feshi a lokacin da ake sa ran ruwan sama domin guje wa wanke abubuwan gina jiki daga gonaki.
Haka kuma ta gargadi mutane da su rika cire kayan lantarki daga soket, su nisanci manyan bishiyoyi, sannan ta shawarci kamfanonin jiragen sama su nemi rahoton yanayi na filayen jirage kafin su tashi.













































