NDLEA ta kama mai samar wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi bayan ya tsere a jihar Neja

WhatsApp Image 2025 12 14 at 10.48.14 750x430

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta kama Mohammed Sani mai shekaru 33 wanda aka fi sani da Gamboli, wanda ake zargi da kasancewa babban mai samar wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Niger, bayan ya tsere wa jami’ai tsawon makonni uku.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jami’an NDLEA sun kai samame gidansa da ke Anguwan Makera a Kuta ranar 20 ga Nuwamba 2025, inda suka kwato kilo 471.8 na skunk, nau’in tabar wiwi, sai dai ya tsere a lokacin.

Bayan samun sahihin bayanan sirri, jami’an hukumar sun sake bibiyarsa tare da kama shi a wani gidan sayar da miyagun ƙwayoyi da ke Anguwan Fadama a Kuta ranar 11 ga Disamba 2025.

Bayanin da daraktan yaɗa labarai da wayar da kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya nuna cewa bincike ya tabbatar Gamboli na taka muhimmiyar rawa wajen samar wa ‘yan bindiga miyagun ƙwayoyi a yankin Shiroro, lamarin da ke taimaka musu wajen aikata laifuka.

Karanta: Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana dalilan zanga-zangar 17 ga Disamba kan matsalar tsaro

A wani samame daban, jami’an NDLEA a jihar Abia sun gano wata masana’antar sirri ta sarrafa maganin tari mai dauke da codeine a ƙauyen Amapu Igbengwo da ke Osisioma, inda suka kwato kwalabe 9,015 masu nauyin kilo 1,152.2.

Haka kuma a jihohin Enugu da Oyo an kama mutane da dama tare da kwace skunk, Colorado, methamphetamine da sauran miyagun ƙwayoyi masu yawa.

A jihohin Ogun, Ondo, Edo da Gombe, jami’an NDLEA sun gudanar da samame da dama inda suka kama mutane da miyagun ƙwayoyi ciki har da tramadol da skunk masu nauyi daban-daban.

A tashar jiragen ruwa ta Apapa a Lagos kuma, an dakatar da shigowar kwalabe 170,000 na codeine syrup masu nauyin kilo 23,579 yayin binciken haɗin gwiwa da jami’an kwastam da sauran hukumomin tsaro.

Bugu da ƙari, hukumar ta ci gaba da shirye-shiryen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi ta hanyar wayar da kan jama’a a makarantu, wuraren ibada, wuraren aiki da al’umma a sassa daban-daban na ƙasar.

Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya, ya yabawa jami’an jihohin da suka yi nasarori tare da ƙarfafa su da sauran jami’an ƙasa da su ci gaba da wannan tsari na daidaito wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here