Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon fashewar iskar gas da ta afku a kauyen Ijarawa da ke karamar hukumar Bichi a jihar.
Wani mutum daya ya tsira daga lamarin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Litinin a Kano.
Ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar 8 ga watan Fabrairu.
“Mun samu kiran gaggawa daga Insifeto Daiyabu Tukur da karfe 07:46 na safe cewa wata mota da ke dauke da silindar gas din girki ta fadivkan hanya kuma daya daga cikin silinda ya fashe.
“Bayan samun labarin, mun hanzarta aika tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 8:00 na safe domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.
Ya ce motar J5 mai lamba FB 52 LAD ta kasuwanci ce ta nufi Katsina daga Kano kuma tana jigilar iskar gas din girki.
Abdullahi ya ce hatsarin ya rutsa da mutane biyu, Maikano Muhammad mai shekaru 45, wadanda ya mutu yayin da Abdullahi Usman mai shekaru 40, an ceto shi da ransa.
An mika dukkan wadanda abin ya shafa ga Usman Usman na ofishin ‘yan sanda na Bichi.
“Ana binciken musabbabin lamarin,” in ji shi.
Jami’in hulda da jama’a ya yi kira ga direbobin da ke dakon abubuwan masu hatsari da su kara taka-tsantsan wajen hada kaya tare da yin tuki cikin kulawa domin gujewa afkuwar hadurran tituna.













































