Majalisar Dattawa ta amince da bukatar shugaban ƙasa Bola Tinubu na tura dakarun Najeriya zuwa jamhuriyyar Benin domin aikin wanzar da zaman lafiya, bayan an samu yunƙurin juyin mulki da ya gaza a ƙasar da ke makwabtaka.
Majalisar ta shiga zaman kwamitin gaba ɗaya bayan ta karɓi wasiƙar shugaban ƙasa tare da gaggauta tattaunawa, inda jagoran majalisa Sanata Opeyemi Bamidele, APC Ekiti ta tsakiya, ya nemi a dauki matakin nan take kan bukatar.
Bayan zaman da bai dauki lokaci ba, majalisar ta dawo zaman bai-daya ta kuma amince da bukatar tura dakarun cikin gaggawa, a cewar majalisar don dakile yawaitar laifuka da lalacewa sakamakon yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon.
A yau shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike da wasiƙa ga majalisa inda ya nemi amincewarta bisa tanadin sashe na 5(5) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka gyara, yana mai bayyana cewa bukatar ta zama dole ne saboda rawar da Najeriya za ta taka wajen samar da zaman lafiya ga ƙasar ƙetare da ke neman taimakon gaggawa.
Karanta: Tinubu ya nemi sahalewar majalisar Dattawa kan tura sojoji zuwa Jamhuriyar Benin
Shugaban ƙasa ya nuna cewa ƙasar Benin ta nemi tallafin gaggawa na goyon bayan jirage masu saukar ungulu da kuma dakarun Najeriya, la’akari da alaƙar zumunci, makwabtaka da ƙa’idar tsaro tare a tsakanin ƙasashen yankin da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ECOWAS take karewa.
Majalisar ta kara da cewa halin da gwamnatin Benin ke ciki bayan yunƙurin karɓe iko ba bisa ka’ida ba na buƙatar hanzarin taimako daga wajen ƙasashen da ke da alaƙa ta tarihi da tsaro da ita, tare da tabbatar da cewa bukatar ta cancanci amincewa cikin gaggawa.
A baya-bayan nan sojojin da ke ƙarƙashin “kwamitin soji na sake tsari” ƙarƙashin Laftanar Kanal Pascal Tigri sun mamaye gidan talabijin na gwamnati a Cotonou, inda suka sanar da kifar da gwamnatin Patrice Talon, amma an tarwatsa yunkurin bayan dakarun Najeriya da jiragen yaki sun shiga cikin lamari a makwabciyar ƙasa.













































