Ma’aikatan jami’o’i sun ƙuduri shiga yajin aiki a Najeriya

Jami'ar, ABU, Zaria, jami'oi, yajin aiki, Najeriya
Ƙungiyar manyan ma'aikatan Jami'oin Najeriya, SSANU da kuma ta ma'aikatan jami'a da basa koyarwa, NASU sun ce za su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin mai...

Ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’oin Najeriya, SSANU da kuma ta ma’aikatan jami’a da basa koyarwa, NASU sun ce za su tsunduma yajin aiki a ranar Litinin mai zuwa.

Ƙungiyoyin sun cimma matsayar a ƙarshen wani taron da suka kammala a ranar Lahadi a birnin Akure na jihar Ondo da ke kudancin ƙasar.

SSANU da NASU sun ce za su shiga yajin aikin na gargaɗi na kwana bakwai ne domin neman gwamnati ta biya musu wasu haƙƙoƙinsu.

Karin labari: Ramadan: ‘Yan kasuwa a jihar Kano sun koka kan karancin ciniki

Ciki har da rashin biyan albashinsu na wata 4 da gwamnatin ƙasar ba ta yi ba na lokacin da suka shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya, a shekarar 2022.

Ƙungiyoyin sun nuna rashin jindaɗinsu kan rashin biyan mambobinsu albashin duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta biya takwarorinsu na malaman jami’oi nasu kuɗaɗen.

Shugaba Bola Tinubu tuni ya bayar da umarnin a biya ma’aikatan jami’oin kuɗaɗensu da aka yi, sai dai ƙungiyoyin na cewa har yanzu basu gani a ƙasa ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here