Likitocin masu neman ƙwarewa sun roki gwamnantin tarayya ta biya su kudaden horo

doctors

Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa (NARD) ta roki Gwamnatin Tarayya da ta biya kudaden alawus alawus na horar da maiakatan lafiya da aka yi a 2023 da 2024.

Shugaban kungiyar Dr Osundara Tope-Zenith ne ya yi wannan kira a wani taron manema labarai ranar Asabar a Abuja.

Taron dai an yi shi ne domin kawo karshen taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) da taron Kimiyya na kungiyar na 2025.

Tope-Zenith ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan rashin biyan basussukan da suke bi wadanda aka yi wa gyaran fuska na tsarin albashi mai tsoka (CONMESS)

Sai dai ya yabawa ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya bisa kiran taron masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin da suka shafi MRTF.

“majalisar zartarwar kungiyar (NEC) ta lura da yadda ‘yan kungiyar suka ci gaba da yin aiki har tsawon shekaru biyar da suka gabata amma babu wani gyara da aka yiwa albashi da alawus alawus.

“Wannan karara ce ta saba wa tanadin yarjejeniyar hadin gwiwa ta 2009, sai dai ta nuna damuwarta kan yadda ake fama da karancin ma’aikata a yawancin asibitoci.

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta biyan basussukan da aka yi wa kwaskwarima da kuma biyan sauran basukan albashi ba tare da bata lokaci ba.

Tope-Zenith ya kuma bukaci a aiwatar da cikakken gyare-gyaren da aka samu na mafi karancin albashi na 2019 da 2024 kan albashin likitoci da ma sauran alawus-alawus.

Sai dai ya ce idan har bayan makonni shida ba a samu wani muhimmin martani ba, hukumar za ta kira taron gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here