An yanke wa Dr John Abebe, suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo hukuncin daurin shekaru bakwai saboda almundaha da ‘kirkirar karya’. Mai shari’a Mojisola Dada na kotun laifuka na musamman ta Ikeja ta bada hukuncin a ranar Asabar amma da zabin biyan tarar Naira miliyan 50 da za a biya cikin kwana 30.
Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Abebe, wanda kani ne ga tsohuwar first lady, Stella Obasanjo a kotu kan zarginsa da ‘kirkirar karya’. A tuhumar, EFCC ta yi ikirarin cewa Abebe “da sane ya kirkiri” wata takarda ta ranar 30 ga Nuwamba, 1995 da BP Exploration Nigeria Limited ya rubuta zuwa ga Inducon Limited. Alkalin ya yanke hukuncin ne bayan mai shigar da kara ya tabbatar da hujja kan zargin kuma aka yanke hukuncin da ya da ce.
A cewar EFCC, Dr Abebe kuma ya yi kokarin hana doka yin aikinta ta hanyar gabatar da wasikar bogi ta ranar 30 ga watan Nuwamban 1995 ‘a matsayin hujja’ a kotu a kara mai lamba FHC/L/CS/224/2010 tsakanin Dr John Abebe da Inducon Nigeria Limited da Statoil Nigeria Limited.
Hakazalika, kamfanin man fetur mai suna Statoil Nigeria Limited a ranar 22 ga watan Yunin shekarar 2010 ta kuma zargi Dr Abebe ta kirkirar takardar bogi.
Statoil Nigeria Limited ta yi zargin cewa wanda aka yi karar ya kirkiri wasu sassan yarjejeniya na raba riba (Net Profit Interest Agreement (NPIA) mai dauke da kwanan wata na 30 ga watan Nuwamban 1995 da British Hakazalika, kamfanin man fetur mai suna Statoil Nigeria Limited a ranar 22 ga watan Yunin shekarar 2010 ta kuma zargi Dr Abebe ta kirkirar takardar bogi, rahoton The Nation.
Statoil Nigeria Limited ta yi zargin cewa wanda aka yi karar ya kirkiri wasu sassan yarjejeniya na raba riba (Net Profit Interest Agreement (NPIA) mai dauke da kwanan wata na 30 ga watan Nuwamban 1995 da British Petroleum (BP) ya rubuta.













































