Kano: Garin kwacen waya mota ta buge matashi ya mutu

Mai kwacen waya
Mai kwacen waya

A daren lahadi ne wani matashi ya zare makami (‘Dan bida) ya yiwa wata mata barazana tare da karbe wayar da ke hannunta a tititn Zoo Road da ke yankin gandun albasa a Karamar Hukumar Birni.

Karanta wannan: Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 28.9

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, matashin mai kimanin shekaru 25, ya tsallaka titin ne don ya kwaci wayar da ke hannunta, kuma ba’a san ko dan wanne yanki bane a cewar shaidun gani da ido.

Sai dai gadon bayan matashin ya karye (spinal code disconnection) kuma kan sa ya fashe, an kai shi sashen bada kulawa ta musamman.

Karanta wannan: Cikin hotuna: Dubban magoya baya sun tarbi Gwamnan Kano Abba Kabir bayan hukuncin kotun koli

kazalika an gano cewa matashin yaji raunuka da dama, wanda kokon kansa ya fashe haka kuma kashin bayansa ya karye.

Cikin wani rubutu da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafin sa na Fesbuk, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ana dai kallon cewa ba wannan ne karo na farko da masu kwacen waya ke cin karensu ba babbaka a wasu hanyoyi ko tituna ba, wanda hakan wani babban kalubale ne mai zaman kanshi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here