Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana godiyarsa ga ‘yan Najeriya da shugabannin yankin bisa nuna damuwa da kauna a lokacin da ake rikicin siyasa a ƙasar guinea-bissau, yayin da yake can yana sa ido kan zaɓe.
Jonathan ya yi wannan bayanin ne ga manema labarai a Abuja bayan dawowarsa daga Guinea-Bissau, inda ya makale na ɗan lokaci sakamakon juyin mulki da aka yiwa gwamnatin shugaban ƙasar, Umaro mbalo.
Jonathan ya ce ya ga dacewa ya yi magana kai tsaye domin ya gode wa ‘yan Najeriya bisa yadda suka nuna damuwa, ganin cewa lokacin da aka samu labarin juyin mulkin, jama’a daga kowane yanki da addini sun nuna tashin hankali da damuwa.
Ya kuma yi godiya ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma shugaban ƙasar ivory coast, Alassane Ouattara, bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da dawowarsa lafiya Najeriya.
Jonathan ya bayyana cewa an dawo da shi ne ta jirgin ivory coast saboda gwamnatin ƙasar ta samu izinin saukar jirgi da wuri fiye da Najeriya, duba da makusanciyar dangantaka tsakanin ƙasashen francophone, wanda ya sa jirgin Ivory Coast ya isa kafin na Najeriya.
Ya ce daga jin cewa jirgin Najeriya zai taso, ya nemi a dakatar da shi domin kada a yi wahalar banza, ganin cewa jirgin Ivory Coast ya riga ya iso domin ɗaukarsa.
Rikicin siyasar Guinea-Bissau ya barke ne bayan zaɓen shugabanci da majalisar dokoki na ranar 23 ga watan nan, wanda aka ce ya kasance mai matuƙar zafi tsakanin shugaban ƙasa mai ci, Umaro mbalo, da abokin takararsa, Fernando Dias.
Karanta: DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan maganganun da ake kallon za su iya tayar da hankali
A ranar 26 ga watan nan ne rikicin ya ƙara tsananta, yayin da aka ji karar harbe-harbe a kusa da fadawar shugaban ƙasa da hedikwatar hukumar zaɓe.
Daga bisani shugaban ƙasar ya sanar cewa an kifar da gwamnatinsa kuma an kama shi, kodayake ya ce ba a yi amfani da karfi a kansa ba.
Bayan haka wasu jami’an soja da suka bayyana kansu a matsayin “kwamandan sojojin farfaɗo da tsaron ƙasa da oda” sun bayyana a talabijin na gwamnati, suna sanar da karɓar mulki tare da dakatar da dukkan cibiyoyin siyasa.
A cikin wannan rudani ne fargabar tsaro kan Jonathan da tawagarsa ta karu, amma daga ƙarshe sun dawo Najeriya Lafiya a ranar alhamis.
NAN













































