Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana Alhaji Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.
Jami’in dake tattara sakamakon zaɓen Jihar ta Sokoto Farfesa Armaya’u Hamisu, shi ne ya bayyana hakan bayan kammala tattara sakamakon zaben daga kananan hukumomi 23 na jihar, ranar Lahadi a Sokoto.
Hamisu, wanda shi ne shugaban jami’ar tarayya dake Dutsin-ma, ya ce Aliyu ne ya lashe zaben da kuri’u dubu 453 da 661.
Ya ce Malam Sa’idu Umar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu da kuri’u dubu 404 da 632.
Ya ce jam’iyyu 17 ne suka fafata a zaben, wadda a cewar sa daga cikin masu kada kuri’a miliyan 2 da dubu 172 da 56 a jihar, an tantance mutane dubu 901 da 513.
Jami’in zaben ya ce an kaɗa kuri’u dubu 864 da 419 da aka amince da su yayin da aka soke ƙuri’u dubu 15 da 357.
Hamisu ya ce an gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada.













































