Sakamakon ci gaba da sauye-sauye da aka samu a fannin kimiya da fasaha, musamman bangarorin tafiyar da harkokin aikin noma, Jami’an ƙungiyar WOFAN sun halarci bita ta mussaman a kasar Dubai kan amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wadda a turance ake kira da Artificial Intelligence (AI) domin inganta ayyukan su da samar da isasshen abinci mai inganci da kuma samar da mafita kan matsalolin da suka shafi canjin yanayi da kuma samar da aikin yi ga matasa.
Wakilin Solacebase wanda ke cikin tawagar ya ruwaito cewa taron, wanda aka gudanar daga ranar 25 ga watan Janairu zuwa 27 ga watan Janairu, 2024, ya tattaro mahalarta daga kasashe shida ciki har da Najeriya, Pakistan, Tanzania, Morocco, Sri Lanka, da Habasha.
Kuma taron ya mayar da hankali kan aikace-aikacen fasahar AI a cikin aikin noma da taimakon manoma wajan gudanar da aikin su cikin sauki tare da inganta ayyukan su.
Da take jawabi a wajen taron, Daraktar WOFAN-ICON2 kuma Jakadiyar zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya, Dr. Salamatu Garba, ta jaddada cewa horon ya yi daidai da manufofin WOFAN-ICON2 na samar da mafita mai ɗorewa, da kuma inganta rayuwar mata da manoma da kuma samarwa da samari aikin yi.
Ta kuma ce, horon zai baiwa mahalartansa wadanda duk matasa ne damar fahimtar sabuwar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta Artificial Intelligence (AI) tare da zurfafa fahimtar su wajan gudanar da aikin e-extension services wanda zai basu damar samun aikin yi da kuma samar da abinci mai dorewa.
Da yadda e-extension na AI zai inganta ayyukan noma, da daidaita tsarin sarrafa albarkatu, da samar da mafita ga manoma.
“Har ila yau, shirin ya nuna mahimmancin shigar da matasa a cikin sababbin shirye-shirye na amfani da fasahar AI, tana mai jaddada cewa samun bunkasar fasahar sadarwa zai zama mahimmi wajen samun aikin yi a nan gaba.”
A jawabinsa na bude taron, babban jami’in gudanarwar na Prospect Development Services, Bayode Hambolu, ya yabawa yadda WOFAN ke bibiyar dabarun ci gaba na AI.
Ya ce, tabbas akwai haske game da yuwuwar samun canji ta hanyar amfani da fasahar AI a cikin masana’antu, musamman a aikin gona da sauran wuraren aiki.
A nata bangaren ƙwararriyar a fannin amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta Artificial Intelligence (AI) da ba da shawara, Dakta Katarina Beta, kuma guda daga cikin wadanda suka bad horon, ta ba da haske game da dama da ƙalubalen da kuma damarmakin da AI ke bayarwa a ɓangarorin ayyukan yau da kullum.
A cewar Dakta Beta, AI na samar da sabbin damammaki a fannoni kamar nazarin bayanai, shirye-shirye, bangaren injiniyanci, kiwon lafiya, fasahar sadarwa, tsaro ta internet, da inganta aikin gona.
Sai dai ta bukaci mahalarta horon su rungumi fasahar AI a matsayin abokin aiki don ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, tare da jaddada buƙatar ci gaba da ilmantarwa da don ci gaba da dacewa a cikin duniyar fasahar AI.
A zantawar mahalarta horon da SolaceBase sun nuna jin dadinsu ga horon da suka samu, inda suka bayyana cewa ilimin da aka samu zai taimaka a fannonin su.