Jami’a a Kano ta musanta batun kungiyar ASUU kan zargin yaɗa bayanan karya

KUST NEW 3 (1)

Hukumar gudanarwar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano ta musanta zargin da kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, reshen jami’ar, ta yi mata kan watsa bayanan da ba su da tushe.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin rajistara kuma shugaban sashen yada labarai da hulɗa da jama’a na jami’ar, Abdullahi Abdullahi, ya fitar a Kano ranar Asabar.

Tun da farivJaridar Solacebase ta rawaito cewa kungiyar ASUU ta jami’ar ta bayyana aniyar ta na shiga yajin aiki idan bukatunta basu biya su ba, tana zargin shugabancin jami’ar da rashin gaskiya da nuna girman kai.

A martanin jami’ar, hukumar ta bayyana cewa zargin da ASUU ta yi ba shi da tushe, an yi su ne domin yaudarar jama’a kan ci gaban jami’ar da kuma ƙoƙarin da gwamnatin jihar Kano ke yi wajen inganta ilimi.

Sanarwar ta bayyana ayyuka da dama da aka kammala a karkashin jagorancin shugaban jami’ar Farfesa Musa Yakasai, ciki har da gyaran dakunan karatu da aji, shigar da na’urorin koyarwa na zamani, da sabunta tsarin yaɗa sauti a makarantar.

Haka kuma, ta jaddada cewa an tura bukatar karin albashi na kaso 25 da 35 ga gwamnatin jihar Kano domin amincewa, tare da yaba wa gwamnati bisa goyon bayanta ga harkar ilimi.

Jami’ar ta ce, ta gaji lissafin kudi da ba a tantance ba daga shekarar 2020 zuwa 2022, amma ta riga ta ɗauki masu duba kudi domin sabunta bayanan kudi na jami’ar, tana mai cewa zargin ASUU siyasa ce kawai.

Hukumar ta roki jama’a da su yi watsi da bayanan da ASUU ta fitar tare da tabbatar da aniyarta na ci gaba da kare walwalar ma’aikata da ɗalibai da kuma ci gaban jami’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here