Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, ya ce rashin gyaran layin wutar Shiroro-Kaduna-Mando da aka lalata tun Oktoba 2024 ya jefa wutar lantarkin kasar cikin matsala.
Ya bayyana cewa layin na daya daga cikin manyan layukan da ke isar da wuta zuwa arewa, amma matsalar tsaro ya hana gyaransa.
Ministan ya kara da cewa ana shirin kashe biliyan N36 wajen raba transfoma a shiyyoyi shida da kuma sanya fitilun hasken rana da na’urar CCTV a tituna don dakile masu lalata kayayyakin gwamnati.
A shekarar 2025, an ware Naira tiriliyan biyu ga ma’aikatar, inda za a yi amfani da Naira biliyan 700 don rage gibin mita na wuta da kara inganta tsarin biyan kudi.