Hedikwatar tsaro ta yi watsi da zargin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi wa sojoji game da harin da aka kai gidan gyaran hali na Kuje da kuma harin da aka kai kan jirgin fasinjan Kaduna zuwa Abuja a baya.
Daraktan yada labaran Hedikwatar, Manjo Janar Jimmy Akpor, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya bayyana zargin da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode, ya yi a matsayin wani abin ban tsoro da kuma rashin tabbas.
Akpor, ya ce Fani-Kayode ya yi zarge-zarge a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sada zumunta na internet biyo bayan yawaitar hare-haren ta’addanci musamman harin da aka kai a gidan gyaran hali na Kuje.
Ya ce Fani-Kayode ya kuma yi ikirarin cewa an janye sojoji jim kadan kafin a kai wa gidan gyran halin hari.
“Mai yiyuwa ba zai yiwu ba cewa irin wannan da’awar wani bangare ne na yunkurin da aka kididdige na haifar da rarrabuwar kawuna da adawa tsakanin dukkan hukumomin gwamnati da suke yin aiki tare don magance matsalolin rashin tsaro a ƙasar.
Kakakin tsaron ya ce Fani-Kayode ya kuma yi ikirarin cewa sojoji ba su dauki wani mataki ba kan harin da ‘yan ta’addan Shiroro suka kai a baya-bayan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji da ‘yan sanda da fararen hula.
Ya ce hakan kuma wani yunkuri ne na bata wa soji suna da haifar da cece kuce tsakanin jami’an tsaro da kuma babban hafsan sojin kasar nan.













































