Har yanzu nine shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP — Tambuwal

Aminu Tambuwal 678x381 1
Aminu Tambuwal 678x381 1

Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan jihar Sokoto ya musanta cewa ya sauka daga mukaminsa na shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP.

Tambuwal dai yanyi takarar shugaban kasa a PDP kafin ya janye wa Atiku Abubakar a zaɓen fidda-gwani na jam’iyyar.

Dailynigerian ta rawaitu cew ya ƙaryata rahoton wata sanarwar da Darakta-Janar na ƙungiyar, CID Maduabum ya fitar a yau Juma’a.

“Ina mai sanar da jama’a da masu ruwa da tsaki a PDP cewa shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP (PDP-GF), Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal. Sabanin rahotannin kafafen yada labarai, Aminu Waziri Tambuwal bai ajiye mukaminsa na shugaban kungiyar ba.

“Mambobin kungiyar Gwamnonin PDP suna aiki a bayan fage don warware duk wata takaddama da ta shafi jam’iyyar. Za a gudanar da taron ƙungiyar nan ba da jimawa ba,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here