Eid-elfitr: Ganduje ya haramta daga tutocin siyasa a masallatan Idi

Ganduje Sallah baba 678x381 1
Ganduje Sallah baba 678x381 1

Gwamnatin Kano ta haramta lika hotuna da daga tutucin siyasa a lokacin bukukuwan karamar Sallah.

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayyana hakan ta cikin sakonsa na barka da Sallah ga al’ummar Kano.

Ta cikin sakon barka da Sallar da Gwamnan ya fitar ta hannun Kwamishinan yaɗa labara na jihar Malam Muhammad Garba, ya ce daga yanzu an hana saka tutoci, ko allunan yan siyasa yayin sallar idi da sauran bukukuwan sallah domin kaucewa rikici.

Ya ce, Sallar idi ibada ce muhimmiya bayan azumin Ramadana da ake bin bayanta da bukukuwan bajakolin tarihi da al’adu, wanda ake zuwa kallo har daga kasashen waje.

Kazalika Gwamnan yace bai kamata a mayar da wuraren Ibadah wajen gangamin siyasa da yakin neman zabe ba.

Gwamna ya jaddada cewa, daga allunan siyasa a yayin taron da ya hada jama’a masu mabanbantan ra’ayi kamar Hawan Daushe, ka iya haifar da tarzoma.

Sanarwar ta kuma umarci yan siyasa da su tabbatar sun yi biyayya ga sabuwar dokar zabe.

Gwamna Ganduje ya taya al’ummar musulmi murnar bikin Sallah, tare da fatan za su yi riko da abin da suka koya a watan azumi.

Sannan ya yi kira ga jami’an tsaro da su nuna halin ba sani ba sabo, ga duk wanda ya yi kokarin tayar da zaune tsaye yayin bukukuwan sallar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here